Koma ka ga abin da ke ciki

Baza Kolin da Aka Yi a Treasure City “Kyauta” Ce Daga Allah

Baza Kolin da Aka Yi a Treasure City “Kyauta” Ce Daga Allah

Birnin Cluj-Napoca wanda aka fi sani da The Treasure City yana cikin manyan birane a ƙasar Romania. Kuma a lokacin da aka yi baza kolin littattafai da aka kira Gaudeamus daga ranar 20 zuwa 24 ga Afrilu, 2016, Shaidun Jehobah sun bayyana wa mutane irin abubuwa masu tamani da za a iya samu a cikin Littafi Mai Tsarki. Sun kafa rumfa a wurin baza kolin kuma suka yi wa dubban mutanen da ke son bidiyonmu da kuma littattafai da kuma Littafi Mai Tsarki da suka baza wa’azi.

Makarantu da yawa sun zo wurin da aka baza kolin, kuma malamai da yawa sun kawo dalibansu rumfar Shaidun. Daliban sun ji dadin kallon bidiyoyin Ka Zama Abokin Jehobah, kuma da yawa daga cikinsu sun so a ba su Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki da kuma kasidar nan Ku Koyar da Yaranku. Wata ma da take aikin kula da yara da aka nuna wa bidiyon ta ce wa ‘yar’uwata, “Muna bukatar mu rubuta sunan wannan dandalin [wato www.jw.org]” don mu nuna wa yaran bidiyoyin.

Matasa a cikin daliban sun ji dadin kallon bidiyoyin zanen allo da aka nuna musu a na’ura. An nuna musu bidiyoyin nan Soyayya ta Gaskiya Ce ko ta Karya? da Ka Zama Mai Hikima a Dandalin Zumunta na Intane da kuma bidiyon Ka Bugi Azzalumi Ba Tare da Damtse Ba.

Wani Firistin cocin Orthodox da matarsa sun ziyarci rumfar, kuma suka karbi Littafi Mai Tsarki na New World Translation of the Holy Scriptures da kuma wasu kasidu. Firist din ya ce fihirisar da ke Littafi Mai Tsarkin ya burge shi sosai. Ban da haka ma, ya ji dadin yadda mafassaran suka yi kaulin mutane da kuma littattafan da aka tabbata da su. Ya ba wa Shaidun lambar wayarsa kuma ya ce su kira sa don su tattauna game da Littafi Mai Tsarki.

Matar firist din ta tambayi Shaidun a ina ne a dandalin jw.org za ta iya samun abubuwan da yara za su yi nazarinsa. Sai aka gaya mata ta je sashen “Yara” a dandalin. Bayan an nuna mata bidiyoyin nan Ku Faɗi Gaskiya ta ji dadin kallon bidiyon. Ban da haka ma, aka nuna musu wasu bidiyoyin da kuma wasu abubuwa a dandalin, sai mijinta ya ce: Wannan “kyauta” ce da Allah ya ba wa mutane.