Koma ka ga abin da ke ciki

Amalanken Wa’azi a Wuraren Hutu na Kasar Jamus

Amalanken Wa’azi a Wuraren Hutu na Kasar Jamus

A wasu manyan birane a duniya, mutanen da suke yawan wucewa da kafa sun san cewa Shaidun Jehobah sukan tsaya da amalanken wa’azi cike da littattafansu. Alal misali, a Jamus Shaidun Jehobah suna da wurin da suke tsayawa a birnin Berlin da Cologne da Hamburg da Munich da kuma wasu birane.

Amma idan suka je wasu kauyuka ko wuraren da ake zuwa hutu a kasar Jamus fa, za su sami sakamako masu kyau kuwa? Za a iya amfani da amalanken wa’azi a arewacin kasar da wasu wuraren da suke kusa da kogi da kuma tsibirai kuwa? A shekara ta 2016, ofishin Shaidun Jehobah da ke Tsakiyar Turai ta shiri na musamman da zai amsa tambayoyin. Daga Mayu zuwa Oktoba, Shaidun Jehobah guda 800 suka ba da kai don su je su kafa amalanken wa’azi a wurare 60 a arewacin Jamus.

“An Soma Daukan Mu a Matsayin ‘Yan Garin”

An marabce Shaidun Jehobah sosai. Wani da ya ba kai ya ce: “Mutanen sun so wa’azinmu, suna da fara’a kuma suna jin dadin tattaunawa da mu a sake.” Wata mai suna Heidi da ta je garin da ake kira Plön ta ce: “Bayan ‘yan kwanaki, mutanen suka soma daukan mu a matsayin ‘yan garin. Wasu sun soma gane mu kuma in sun gan mu sai su daga mana hannu.” Wani kurma ya yi amfani da yaren kurame ya ce: “Kuna ko’ina!” Ya fadi hakan ne don shi da abokansa suna dawowa daga wani taron kurame da aka yi a kudancin Jamus ne, kuma a can ma ya hadu da Shaidun Jehobah.

Wasu ‘yan garin sun taimaka mana. A tsibirin Wangerooge, wani dan sanda a zo ya sami ‘yan’uwanmu kuma ya gaya musu yadda za su iya yin wa mutane da yawa wa’azi. A Waren an der Müritz, wani da yake bi da mutanen a jirgin ruwa ya nuna musu wurare masu ban sha’awa a wurin, sa’an nan ya nuna musu da yatsarsa wurin da aka ajiye amalanken wa’azin kuma ya ce: “A can kuma za ku iya koya abubuwa game da Allah.” Mutane da yawa da suka zo hutu suna zuwa inda aka ajiye amalanken don su karanta abin da ke jikinsa.

Da mutanen garin da wandada suka zo yawon bude ido sun son kasidun nan:

  • Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske? Wani da ya zo yawon bude ido ya ce: “Na dade ina yi wa kaina wannan tambayar. Sai ga shi da na zo hutu zan sami damar karanta amsar.”

  • Albishiri Daga Allah! Wani dattijo ya gaya wa Shaidun Jehobah cewa ya gaji da bin addini. Sai suka taimaka masa ya gane cewa ‘yan Adam ba za su iya magance matsalolinmu ba; amma Allah ne kadai zai iya yin haka. Mutumin ya karbi kasidar kuma ya ce zai karanta.

  • Abin da Na Koya a Littafi Mai Tsarki. Wani uba ya bar ‘yarsa ta dauki kasidar don an wallafa shi ne don yara. Sa’an nan ya dauki Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki kuma ya ce: “Wannan zai taimaka wa iyalina.”

Wadanda suke wucewa sun dauki littattafai 3,600. Mutane da yawa sun ce Shaidun Jehobah su zo su yi nazari da su kuma su ci gaba da tattaunawa da su.

Shaidun Jehobah da suka je irin wannan wa’azin sun ji dadinsa sosai. Jörg da matarsa Marina da suka je kusa da tekun Baltic sun ce: “Wannan babban gata ne.” Kuma sun dada da cewa: “Mun ji dadin ganin halittun Allah da koya wa mutane game da Mahaliccinmu.” Wani mai suna Lukas dan shekara 17 ya ce: “Na ji dadinsa! Kuma na sami damar taimaka wa wasu.”