Koma ka ga abin da ke ciki

Taron Yaren Tagalog a Roma​—“sun sake kasancewa tare kamar iyali!”

Taron Yaren Tagalog a Roma​—“sun sake kasancewa tare kamar iyali!”

Dubban Shaidun Jehobah da suke yaren Tagalog daga kasar Filifin sun yi tafiya mai nisan fiye da kilomita 10,000 don su halarci babban taron da aka yi a watan 24 zuwa 26 ga Yuli a shekara ta 2015 a Roma da ke kasar Italiya.

Binciken da aka yi ya nuna cewa kimanin mutanen Filifin fiye da 850,000 ne suke zama a Turai. Saboda haka, Shaidun Jehobah sun kafa ikilisiyoyi 60 da kuma kananan rukunoni a Turai kuma suna yin taro a yaren Tagalog. Kari ga haka, suna yi wa mutane Filifin da suke yankinsu wa’azi.

Wannan babban taron da aka yi na kwana uku a Roma shi ne taro na farko da wadannan ikilisiyoyin da kuma rukunonin suka halarta a yarensu. Mutane 3,239 ne suka halarci taron kuma sun yi farin cikin marabtar dan’uwa Mark Sanderson wanda daya ne daga cikin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah kuma ya taba hidima a kasar Filifin. Kari ga haka, shi ya ba da jawabi na karshe a duka kwanaki ukun.

“Ya Taba Zuciyata”

Yaya mutum yake ji idan ya halarci taron da aka yi a yarensa? Wata mahaifiya mai suna Eva ta ce: “Ba na jin Turanci sosai, amma halartar taron nan a yaren Tagalog ya sa koyarwa Littafi Mai Tsarki ya taba zuciyata.” Don su iya tafiya daga Sifen zuwa kasar Italiya, ita da ’ya’yanta biyu sun yanke shawarar cewa ba za su rika cin abinci kowane sati a gidan abinci ba, amma za suna yi hakan sau daya a wata. Eva ta sake cewa: “Wannan shawarar da muka yanke ta dace domin na fahimci kome a wannan taron.”

Don ta samu ta halarci taron, Jasmin da take zama a Jamus ta nemi izinin daukan hutu daga wurin aikinta. Amma ta ce: “Kafin in tafi, an gaya mini cewa ba zan iya daukan hutun ba domin akwai aiki da ya kamata mu gama, sai na natsu kuma na yi addu’a ga Jehobah kuma na koma wajen shugaban aikina. Sai muka sake tsara aikin, kuma hakan ya taimaka mini in halarci taron. Haduwa da ’yan’uwa maza da mata ’yan Filifin da suka zo daga Turai ya sa ni farin ciki sosai.”

Babu shakka, mutanen Filifin da suke Turai suna kewar gida da kuma abokansu da suke wasu bangarori dabam-dabam a kasar Turai. Wannan taron ya taimaka wa mutane da yawa su hadu da abokansu da kuma ’yan’uwa maza da mata. (Matta 12:48-50) Fabrice ya ce: “Haduwa da mutanen da na sani ya sa ni farin ciki sosai!” A karshen taron wata ’yar’uwa ta ci gaba da cewa: “Mun sake kasancewa tare kamar iyali!”