Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Shaidun Jehobah Sun Taimaka Wajen Tsabtace Birnin Rostov-on-Don

Shaidun Jehobah Sun Taimaka Wajen Tsabtace Birnin Rostov-on-Don

A ranar 20 ga Mayu na shekara ta 2015, shugaban gwamnatin kudancin birnin Rostov-on-Don da ke Rasha, ya tura wa Shaidun Jehobah wasikar godiya “don irin aikin da suka yi na tsabtace birnin.”

A lokacin da mutanen yankin Rostov-on-Don suka fito don su tsabtace garin, Shaidun Jehobah daga ikilisiyoyi guda hudu ma sun fito kuma suka kwashe datti da ke kan hanya da kuma wanda ke bakin kogin birnin. Cikin sa’o’i kadan suka cika buhu 300 da shara kuma daga baya suka yi amfani da manyan motoci don su zubar da sharan.

Me ya sa Shaidun Jehobah suka fito don su taimaka wajen share birnin? Wata ‘yar’uwa mai suna Raisa da ke da shekara 67 ta ce, “ba zan iya cewa ba zan saka hannu a aikin share birninmu ba, domin ina son kowa ya ji dadin zama a cikinsa. Ko da mutane kadan ne kawai suka san abin da muka yi, na ji dadin yin aikin kuma na san cewa Jehobah ya ga aikin da muka yi.” Aleksander ya dada cewa: “Ba kawai wa’azi muke yi wa mutane ba amma muna yin aikin da zai taimaka musu, yin hakan yana sa ni farin cikin sosai.”

Mutanen da suka ga irin aikin da Shaidun Jehobah suka yi, sun yi murna. Wani da yake zama a wurin ya yi mamakin sanin cewa ba a biyan Shaidun Jehobah don wa’azin da suke yi. Daga baya mutumin ya yanke shawarar yin aikin share birnin tare da su, kuma ya ce: “Ban taba tunanin cewa zan ji dadin yin wannan aikin sharan ba!” Kuma ya kara cewa: “Wasu daga cikinku ba sa zama a nan, amma kun saka hannu don share wajen nan tare da mu.”

Wani ma’aikacin gwamnati a birnin ya ga cewa wani karamin rukuni na Shaidun Jehobah sun fi kwashe sharan. Sai ya dauke su hoto kusa da buhunan sharan don ya “nuna ma wasu yadda ya kamata su yi aikin.”