Kowace rana, fursunoni da ke gidajen kurkuku a Amirka suna rubuta wasiku da yawa zuwa ga rassan Shaidun Jehobah don neman taimako game da sanin Allah.

Muna taimakawa ta wajen tura masu koyar da Littafi Mai Tsarki daga ikilisiyoyin da ke yankunan don su ziyarci kuma su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da wadanda ke kurkuku, gidajen yari, gidajen tsare kangararrun matasa da ’yan kwaya da kuma masu shaye-shaye.

A wasu gidajen kurkuku, Shaidun Jehobah suna gudanar da taron ikilisiya a kai a kai. Alal misali, a wani gidan kurkuku, mutane 32 ne suka halarci jawabi ga jama’a da aka bayar a harabobi biyu na gidan kurkukun.

Wannan shiri na taimaka wa fursunoni ya kawo sakamako mai kyau. Wani mutumin da aka same shi da laifin kisan kai kuma aka yi masa daurin rai da rai a jihar Indiana, ya yi gagarumar canje-canje a rayuwarsa kuma aka yi masa baftisma ya zama Mashaidin Jehobah.

Wani Mashaidin Jehobah da ya yi nazari da wani fursuna dabam da ke wani babban gidan kurkuku a jihar California, ya yi bayani game da wannan fursuna, kuma ya ce: “Na san halayensa kafin ya fara nazarin Littafi Mai Tsarki. Canje-canjen da ya yi kafin ya cancanci yin baftisma na da ban mamaki sosai.

Fursunoni da yawa sun daidaita rayuwarsu da abubuwan da suka koya daga Littafi Mai Tsarki duk da sanin cewa hakan zai iya sa ransu cikin hadari. Alal misali, ya zama wajibi a ware wadanda suka daina cudanya da ’yan daba daga sauran fursunoni, ko kuma a kaurar da su zuwa wani gidan kurkuku dabam domin kāre lafiyarsu.

Yadda Littafi Mai Tsarki ya canja rayuwar mutane ya burge ma’aikatan gidan yari sosai. Wasu sun ba da takardun yabo da na aikin ba da kai ga Shaidun saboda aikin mai kyau da suke yi a gidajen kurkuku.