Tun lokacin da aka bude wurin nuna Littafi Mai Tsarki a hedkwatarmu a shekara ta 2013, mutane sun ba da wasu Littafi Mai Tsarki da ba a cika samun su da kuma masu amfani don a kyautata wurin da ake ajiye su. Wadannan Littafi Mai Tsarki sun ƙunshi Complutensian Polyglot da farkon fitowa na fassarar King James da kuma Erasmus’ Greek “New Testament.”