A Yuli na 2009, Shaidun Jehobah sun saya wani fili a ƙauyen New York da shirin ƙaura da hedkwatarsu. Wannan fili yawansa sabon eka 102 ne (253 eka) yana kilomita 80 (wato mil 50) ta arewa maso yamma da na dā ɗin a Brooklyn, New York, inda suke tun 1909.

Shaidun 800 za su zauna kuma su yi aiki a sabon wurin, da zai haɗa da gine-ginen ofisoshi, wajen hidimomi, gidajen kwanciya. Za a haɗa da wani ƙaramin ma’adanar kayayyakin tarihi da ke ɗauke da tarihin Shaidun Jehobah.

Inda za a yi ginin zai ci fili sabon eka 18 (wato, 45 eka) na filin da aka saya, an bar sauran wuraren da suke da itatuwa da wajen fadama kewaye da filin. Ba za a yi gyaran shimfiɗar filin ya haɗa da wuraren da za a iya yanke ciyawar ba. Maimakon haka, za a sa ya yi daidai da wajen da ake da itatuwa.

Masu shirin gini sun shirya yadda ginin ba zai ci lokaci da kuma kayan aiki ba, da zai taimaka a adana mahallin da ba za a kashe kuɗaɗe da yawa ba. Alal misali, za a yi rufin da ciyawa ne da ba za a kashe kuɗaɗe masu yawa ba kuma zai iya tare ruwan sama da kuma yadda ɗakunan za yi sanyi. An shirya ginin ofishin ta fuskar haske don a sami haske a ciki. Abin muhimmanci ne a rage ɓata ruwa.

Me ya sa aka shirya irin ginin nan? Ofisoshin reshe na Shaidun Jehobah a wasu ɓangarorin duniya yanzu suna buga Littafi Mai Tsarki da littattafan da ke bayanin Littafi Mai Tsarki da a dā a Brooklyn kaɗai ake bugawa. A shekarar 2004, an ƙaura da aiki bugawa da kuma tura littattafai daga Amirka zuwa Wallkill, New York, misalin kilomita 145 (wato mil 90) ta arewa maso yamma na Brooklyn.

An kuma yi la’akari da zancen kuɗi. Yin aiki a Brooklyn da kuma adanawa yana cin kuɗi. Idan suka ƙaura zuwa sabon ginin, Shaidu za su iya amfanin kirki da kuɗaɗe don su tallafawa aikin ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki.

Ba a gama da zancen kula da mahalli ba don a ba da izini da za a fara aikin. Idan kome ya yi daidai, za a soma ginin a shekara ta 2013 kuma za a gama shi a shekaru huɗu.

Ban da wajen buga littattafai a Wallkill, New York, Shaidun Jehobah suna da wajen ilimantarwa a Patterson, New York. Ƙungiyar tana da ofisoshin reshe a ƙasashe da yawa. A duk duniya, Shaidun sun kai fiye da miliyan bakwai da rabi.