Koma ka ga abin da ke ciki

Wasiku Daga Wurin Masu Gidan Haya

Wasiku Daga Wurin Masu Gidan Haya

Bai dade ba da Shaidun Jehobah suka kammala aikin fadada ginin Watchtower Farms da ke Wallkill a jihar New York kuma sun yi shekaru shida suna wannan aikin. Da aka kusan kammala ginin, ma’aikatan sun kara yawa, don hakan an bukaci masaukin da za su zauna. Saboda haka, an samo musu gidajen haya guda 25 kusa da wajen.

’Yan haya

Mene ne masu gidajen suka ce game da hayar gidajensu da suka ba wa Shaidun Jehobah?

  • Wata da ta ba da gidanta haya ta ce: “Muna farin ciki da wadanda muka ba wa gidanmu haya, ni da mijina muna zama kusa da gidan, kuma muna ganin irin hadin kai da ‘yan hayar suke ba mu da kuma irin kirkin da suke mana.”

  • Wata ma ta rubuta game da wadanda ta ba wa gidanta haya, ta ce: “Mun ji dadin zama tare da su, muna da wurin da aka gina a bayan gidanmu don mutane su rika yin iyo kuma a duk lokacin da muka gayyace su su zo gidanmu, suna zuwa. Kari ga haka, suna daraja mu sosai, mun ji dadin yin tarayya da su kuma za mu yi kewarsu sosai idan suka tafi.” Kuma matar ta dada cewa: “Gaskiya mun ji dadin zama da su sosai.”

  • Wani mai gidan haya ya ce, “Mun yi farin cikin cewa su makwabtanmu ne ba ‘yan haya ba kawai.”

Gidajen Hayar

Mene ne masu gidan hayar suka ce game da yanayin gidajensu bayan ‘yan hayar sun tafi?

  • “Suna biyan kudin hayar a kan lokaci kuma yanayin gidan yana da kyau sosai sa’ad da suka tashi.”

  • Daya daga cikin masu gidan hayar ya ce: “Ina muku da kungiyar ku godiya saboda yadda kuka kula da gidanmu” kuma ya ce bai yi tunanin cewa Shaidu za su tsabtace gidan haka ba.

  • Wata mata ta ce: “Saboda mun amince da kungiyarku, ba mu bukaci karin kudin da za mu yi amfani da shi don mu gyara gidan bayan ‘yan hayan sun tafi ba.” Me ya sa? “Don sun bar mana gidanmu a yanayin da suka same shi.”

  • Bayan wasu Shaidun Jehobah sun yi ma wani mai gidan haya gyara a gidansa. Sai ya ce: “Zan so ku zama ma’aikatana domin idan kuka yi alkawari, kuna cikawa kuma kuna aiki a kan lokaci. Masu mini aikin gyara ba sa cika alkawarinsu kamar yadda kuke yi.”

Furucinsu na Karshe

  • Kafin kudin hayar wani gida ya kare, mutumin da ya ba su hayar ya ce idan Shaidun za su sake yin hayar gidansa, zai “rage musu kudi” don shi ma ya tallafa wa aikin da suke yi.

  • Kari ga haka, wani mutum ya ce: “Za mu yi farin ciki ba wa ‘yan Watchtower gidajenmu in suna bukatar hakan a nan gaba.”