Koma ka ga abin da ke ciki

Rumbun Hotunan Warwick na a (Mayu Zuwa Agusta 2015)

Rumbun Hotunan Warwick na a (Mayu Zuwa Agusta 2015)

A wannan rumbun hotunan, za ka ga ci gabar da aka samu daga Mayu zuwa Agusta 2015, a aikin da ake yi a sabuwar hedkwatar Shaidun Jehobah.

Hoton da ke nuna yadda hedkwata ta Warwick za ta kasance idan aka kammala. Somawa daga hagu:

  1. Gidan Gareji

  2. Wajen Ajiye Mota don Baki

  3. Gidan Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota

  4. Gidan Zama na B

  5. Gidan Zama na D

  6. Gidan Zama na C

  7. Gidan Zama na A

  8. Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

6 ga Mayu, 2015​—Warwick

Wani mutumi yana so ya saka mataci a cikin tafkin Sterling Forest Lake (Blue Lake). Wannan mataciyar za ta tace duk wani dattin da zai shiga wurin da ruwa ke bi da ke can ƙasar tafkin.

6 ga Mayu, 2015​—Gidan Gyare-Gyare da Wurin Ajiye Mota don Mazauna

Masu gini suna zuba kankare a jikin rawanin da ke rufin Ginin Yin Gyare-Gyare. Zuba simintin zai sa aikin ya fi sauri fiye da kafa bangon da aka yi da kankare.

15 ga Mayu, 2015​—Warwick

Wata mai ɗaukan hoto daga Sashen Adana Bayani tana ɗaukan hoton ginin da ake yi. Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana kallon hotunan a kowane mako don ta ga yadda aikin yake ci gaba.

30 ga Mayu, 2015​—Tuxedo

Mata da miji daga kudancin Kalifoniya sun iso don su yi aiki da Sashen da ke Aikin Famfo. Suna cikin ɗarurruwan da suka iso Tuxedo a ranar. A nan ne ake gudanar da ayyukan gine-ginen da ake yi a Warwick. A ranar Agusta ta 1, sabbin ma’aikata guda 707 ne suka iso wurin.

9 ga Yuni, 2015​—Gidan Zama na B

’Yan ƙwangila suna amfani da na’aurar ɗaga kaya don ɗaga bangon da za a kafa. Gidan zama na B shi ne gini na ƙarshe da aka kafa bango da tagodi.

16 ga Yuni, 2015—Gidan Zama na C da D

’Yan ƙwangila sun saka gadar da ta haɗa Ginin B da C.

25 ga Yuni, 2015—Gidan Zama na C

Masu shuka ciyawa suna shifiɗa ciyawa a yammacin ginin.

2 ga Yuli, 2015—Warwick

Masu gini suna yi wa wurin da ruwa ke kwarara gyarar fuska. An gina wurin ne a shekara ta 1950. Gyarar fuskar da ake yi wa wurin zai hana yawan ambaliyar da ake yi a yankin shafar Warwick da maƙwabta.

15 ga Yuli, 2015—Gidan Zama na A

Don rage cunkoson mutane a wurin aikin, waɗanda suke yin fenti da aikin famfo suna aiki har cikin dare. Wasu mutane ɗarurruwa suna some aiki ne daga ƙarfe 3 na rana zuwa ƙarfe 2 na dare.

20 ga Yuli, 2015—Gidan Zama na D

Wata mai gyaran AC tana koya wa wata yadda ake haɗa wurin da iska yake bi.

21 ga Yuli, 2015—Gidan Zama na B

Ana yi wa gadar da ta haɗa Gidan Zama na B da Ginin Yin Gyare-Gyare fenti.

27 ga Yuli, 2015—Tuxedo

Ɗarurruwan mutanen da suke aiki a Warwick suna jiran motocin da za su ɗauke su. Manyan motoci ne suke kai ma’aikatan wurin da ake ginin kuma sune ke dawo da su.

27 ga Yuli, 2015—Tuxedo

Ana yi wa ma’aikata uku aski. Ana yi wa mutane sama da 400 aski a kowane sati a wuraren aski da ke Tuxedo, Warwick, da wurin ajiye kaya a Montgomery.

3 ga Agusta, 2015—Warwick

Ana so a fara zuba kankare a sashen wasu ramukan da aka tona. Waɗannan ramukan guda ɗari da ashirin mai zurfin mita 150 za su riƙa tana da zafi a lokacin sanyi da kuma sanyi a lokacin zafi. Hakan zai rage kuɗin da ake kashewa da kuma gurɓatarwa.

7 ga Agusta, 2015​—Montgomery, New York

Nan ake karɓa da tara kayan aikin da aka sayo. Ana amfani da kayan a Warwick.

14 ga Agusta, 2015​—Tuxedo, New York

Ma’aikata biyu da suke aiki a Warwick (na biyu da na uku daga dama) suna cin abinci da wata iyalin da ke zaune a yankin. Kamar wannan iyalin, iyalai da yawa na Shaidun Jehobah sun saukar da ma’aikata da dama a gidajensu.

17 ga Agusta, 2015​—Wurin Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota

Wata ma’aikaciya tana duba lebur ɗin ƙasa da wata na’ura.

20 ga Agusta, 2015​—Ofisoshi/Wuraren Hidimomi

An saka tagogi a wurin da baƙi za su fara zagaya.

26 ga Agusta, 2015​—Warwick

Tsakanin watan Mayu zuwa Agusta, an tada Gidan Zama na B wanda shi ne gini na ƙarshe kuma yi rufin. An haɗa gada kuma an kammala hanyoyin bi. An kuma fara lebur ɗin ƙasar.