Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

Rumbun Hotunan Warwick na 6 (Maris Zuwa Agusta 2016)

Rumbun Hotunan Warwick na 6 (Maris Zuwa Agusta 2016)

A wannan rumbun hotuna, za ka ga ci gabar da aka samu daga Maris zuwa Agusta 2016 a aikin da ake yi a sabuwar hedkwatar Shaidun Jehobah da kuma yadda mutanen da suka ba da kansu da yardan rai suke tallafa wa aikin da ake yi a wurin.

Hoton da ya nuna yadda hedkwata ta Warwick da aka kammala take. Somawa daga hagu:

  1. Inda Ake Gyara Motoci

  2. Wajen Ajiye Mota don Baki

  3. Gidan Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

  4. Gidan Zama na B

  5. Gidan Zama na D

  6. Gidan Zama na C

  7. Gidan Zama na A

  8. Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

16 ga Maris, 2016​—Wajen da ake aiki a Warwick

Masu gyara fili suna saukar da bishiyoyi da za a dasa a wurin da ake gine-gine a Warwick. An dasa sababbin itatuwa fiye da 1,400 a hedkwatarmu da ke Warwick.

23 ga Maris​—Inda Ake Gyara Motoci

Wadanda suke aiki a Warwick suna tuna da Mutuwar Yesu da Shaidun Jehobah suke yi a kowace shekara a fadin duniya. Adadin mutane 384 ne suka halarci taron a wannan wurin.

15 ga Afrilu, 2016​—⁠Wajen da ake aiki a Warwick

Kafintoci suna saka wundo a babban kofan shiga Bethel da ke Warwick. Masu aiki a kofar za su marabci baki da yin tsaro da lura da yadda motoci suke shiga da kuma fita daga wurin.

19 ga Afrilu, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani mahaifi da dansa suna saka kafet mai kama da tayil a hanyar wucewa a bene na biyu. An yi amfani da wannan kafet mai kama da tayil a wurin da mutane suke yawan wucewa don zai yi saukin canjawa idan ya lalace.

27 ga Afrilu, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Kafintoci suna saka abin da zai raba ofisoshin. Kuma wannan ne zai taimaka musu su san yadda za su tsara filin ofisoshin.

10 ga Mayu 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani ma’aikaci yana tsara ban daki na baki da ke kusa da zauren kuma yana saka abubuwan da za su raba kowanne ban daki.

26 ga Mayu, 2016​—Wajen da ake aiki a Warwick

Ana horar da mutanen da za su rika kashe gobara a kan yadda za su rika yin hakan. Wannan zai taimaka musu su iya kashe gobara da kuma kāre mutane da kuma gidajen Warwick gabaki daya, ban da haka ma, hakan zai sa su rage aiki wa masu kashe gobarar da suke aiki da gwamnati.

30 ga Mayu, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Kafin a soma Ibada ta Safiya wani mai ba da abinci yana nuna wa ma’aikata a Warwick inda za su zauna.

31 ga Mayu, 2016​—Gidan Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

Wata tana amfani da injin yin lebur don ta saka daya daga cikin alamu guda 2,500 da za su rika taimaka wa mazauna da kuma baki don su san hanya.

1 ga Yuni, 2016​​—⁠Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani mai walda yana saka hannun matakalar benen zuwa majami’ar taro. An saka wani bargo don kada wutan waldar ya bata aikin da aka riga aka gama.

9 ga Yuni, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani da yake aiki da Sashen Masu Gyara Bango da Silin yana kammala aiki a hanyar zuwa wajen nunin nan da ake kiran “Faith in Action” da mutane suke zagaya da kansu. Zanen da aka yi a rumbun yana nanata jigon kowane hoto.

16 ga Yuni, 2016​—Inda Ake Gyara Motoci

Ma’aikata suna gyara kasan da aka yi da kankare. Aikin da suke yi a wurin zai sa kankaren da aka zuba ya yi karfi kuma ya dade, kari ga haka, zai zama da saukin sharewa.

29 ga Yuni, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Kafintoci suna saka rufin zaure. Kuma irin rufin nan yana taimaka wa don a samu hasken rana.

29 ga Yuni, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani da matarsa suna saka tayil a hanyar shiga wurin nunin nan mai suna “The Bible and the Divine Name.”

6 ga Yuli, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wata kafinta tana saka daya daga cikin kujeru guda 1,018 a majami’ar taron. Kuma a wannan majami’ar ne iyalin Bethel za su rika yin nazarin Hasumiyar Tsaro da kuma wasu taro.

9 ga Yuli, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Kafintoci da masu gyaran wuta da kuma wasu ma’aikata suna saka wutar alamar marabta baki da ke zaure.

13 ga Yuli, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Ma’aikata guda biyu suna kai wa masu aiki ruwa. Kuma suna yin hakan musamman ma a lokacin zafi don ana karfafa ma’aikata su rika shan ruwa sosai.

19 ga Yuli, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani ma’aikaci yana saka inda za a rika ajiye Littafi Mai Tsarki a wurin nuni mai suna “The Bible and the Divine Name.” A wurin nunin da akwai wani abin da aka yi da ke zagayawa da zai rika nuna wasu Littafi Mai Tsarki da kayan tarihi na dā da suka yi magana game da Littafi Mai Tsarki.

22 ga Yuli, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Da taimakon wani rubutu mai kalar shudi da ke jikin bango, wani kafinta yana manna wani abin da ke nuna kasar Ostareliya da kuma tsibiran da ke Kudu Maso Gabashin Asiya a babbar zaure. Sunan nan Shaidun Jehobah ya bayana kusan sau 700 a yaruka dabam-dabam.

23 ga Yuli, 2016​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Ana kara wayar da kan ‘yan iyalin Bethel game da wasu abubuwa da ke Warwick. Kuma dalilin da ya sa aka yi hakan, shi ne don a marabci wadanda za su yi aiki a wurin kuma a nuna musu abubuwan da za su rika yi don su kāre kansu daga abubuwan da za su iya yi musu rauni.

17 ga Agusta, 2016​—Tasharmu na JW Broadcasting

Ana saka wutan da ke saman wajen mai ba da rahoto a JW Broadcasting. An kauro da yawancin abubuwan da ake amfani da su su ne daga inda suke dā a Brooklyn.

24 ga Agusta, 2016​—Wajen da ake aiki a Warwick

Wani mai gyaran wuta yana saka wani sabuwar alama mai wuta a kofar shigowa. Tun daga 1 ga watan Satumba na shekara ta 2016, aka soma aiki a sashe dabam-dabam a hedkwatarmu a Warwick.