Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Shaidun Jehobah

Hausa

Rumbun Hotunan Warwick na 5 (Satumba 2015 Zuwa Fabrairu 2016)

Rumbun Hotunan Warwick na 5 (Satumba 2015 Zuwa Fabrairu 2016)

A wannan rumbun hotunan, za ka ga ci gabar da aka samu daga Satumba 2015 zuwa Fabrairu 2016 a aikin da ake yi a sabuwar hedkwatar Shaidun Jehobah da kuma yadda mutanen da suka ba da kansu da yardan rai suke tallafa wa aikin da ake yi a wurin.

Hoton da ya nuna yadda hedkwata ta Warwick da aka kammala take. Somawa daga hagu:

  1. Inda Ake Gyara Motoci

  2. Wajen Ajiye Mota don Baki

  3. Gidan Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

  4. Gidan Zama na B

  5. Gidan Zama na D

  6. Gidan Zama na C

  7. Gidan Zama na A

  8. Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

7 ga Oktoba, 2015—Wajen da ake aiki a Warwick

An kera gada kuma ana so a je a kafa ta. An saka taya a karkashin sa’ad da ake saukar da gadan daga mota. Gadan yana hana mutane shiga wuraren da bai kamata su shiga ba.

13 ga Oktoba 2015—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

An shuka wani irin ciyayi da ake kira sedum a rufin gidan kuma ciyayin yakan canja kala kafin lokacin hunturu. An shuka ire-iren wannan ciyayin har goma sha shida a rufin gidan. Irin wannan rufin mai koren kala yana taimakawa wajen rage ruwan sama da ke zubowa a kan rufin kuma hakan zai taimaka wajen sa a rage kuɗin da ake kashewa don kula da mahallin.

13 ga Oktoba , 2015—Gidan Zama na D

Wani kafinta yana gyara kabat a kicin na ɗakunan. A karshen watan Fabrairu na shekara ta 2016, ’yan’uwan da suke aiki a Sashen Kafintoci sun gama kashi 60 cikin 100 na kabat da ake sakawa a cikin dakunan.

16 ga Oktoba , 2015—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Masu aikin wutan lantarki suna saka kwan lantarki da zai rika haskaka tambarinmu na Watch Tower da ke saman hasumiyar.

21 ga Oktoba , 2015—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Ofisoshi da Wuraren Hidimomi, da farfajiyarsu da kuma inda ake karban baki yana haske da daddare. Wannan hasumiyar za ta sa baki su iya ganin dukan wuraren Warwick.

22 Oktoba , 2015—Wajen da ake aiki a Warwick

Masu aikin suna gina wata hanya da motocin za su iya yin amfani da ita idan wani abu na gaggawa ya taso, sai suka gyara wurin kuma suka zuba kankare. Wannan hanya da aka rufe da wani abu na dan lokaci yana rage zaizaya da ake yi a wurin sa’ad da ake aikin.

9 ga Nuwamba, 2015—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Ma’aikata suna saka gilashin a saman lif da ke wajen da ake karban baki. Wannan gilashin guda goma sha daya da aka saka a Ofisoshi da Wuraren Hidimomi yana taimakawa wajen barin hasken rana ya shigo cikin ofisoshin.

16 ga Nuwamba , 2015—Gidan Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

Wani mai walda yana yanka karfen da ruwa mai sanyi zai rika bi zuwa cikin na’aurar da ke sa gidaje sanyi.

30 Nuwamba , 2015—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wata kafinta tana saka abin da zai rike tagar ginin. Bayan ta saka abin da zai rike bangwayen, sai ta saka tagar.

17 ga Disamba , 2015—Wajen aiki a Warwick

A lokacin damuna ’yan’uwan suna saka tayal. A tsakiyan hoton ta dama za ka ga wani filin da aka bari. Motar saukar da kaya tana saukar da tayal da za a sassaka a wurin. Ta hagu an rufe wani sassa don kada zaizaya ta yi barna.

24 ga Disamba , 2015—Wajen da ake aiki a Warwick

Ma’aikata suna dauke da wayar wuta za su kai wajen da aka jawo wutan lantarki da za a yi amfani da shi a Warwick.

5 ga Janairu, 2016—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Wani ma’aikaci ya gama aiki a kan rufin hanyar da ke tsakanin Garejin Baki da Ofisoshi da Wuraren Hidimomi. Wannan rufin zai kāre baki don kada ruwan sama da kankara su taba su.

5 ga Janairu, 2016—Gidan Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

Ma’aikacin wutan lantarki yana saita mashin na tafasa ruwa. An kammala aikin saka mashin guda hudu na tafasa ruwa a Warwick.

8 ga Fabrairu, 2016—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Makanikai suna saka injin busar da kaya a Sashen Wanki. Injunan za su iya daukan kaya mai nauyin kilo 6 zuwa 45. Za a saka injunan wankin kaya a ta hannun hagu na bangon.

8 Fabrairu, 2016—Garin Tuxedo

Dan’uwa Gerrit Lösch memban Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah yana gudanar da nazarin Hasumiyar Tsaro a Bethel kuma masu aiki da suke wurare dabam-dabam a Warwick ma suna saurarawa ta talabijin.

19 ga Fabrairu , 2016—Gidan Zama na A

Sashen Tsara Dakuna suna kai kafet zuwa wani gidan zama. An yi odar kafet fiye da yadi 78,000 da za a yi amfani da shi a Warwick.

22 ga Fabrairu , 2016—Wajen aiki a Warwick

A watan Satumba  2015 da kuma Fabrairu 2016, Shaidun Jehobah sun karbo takardun da zai ba ma’aikata izinin soma zama a Gidan Zama na C da D. Bayan haka, aka sassaka lif a dukan gidajen kuma aka kammala hanyar zuwa gidajen zama da saka tayal. Saboda hunturu an soma gyara mahallin wurin kafin lokacin da ya kamata a yi hakan.

24 ga Fabrairu , 2016—Gidan Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

Wani da yake aiki da sashen masu saka silin yana sa silin kuma abin da ya saka a kafarsa yana taimaka masa don ya kai sama. Sashen Masu Gyara Bango da Silin ne suke saka da kuma yin firam da kula da ita da kuma gina bango da flastar bangon, kuma su ne suke saka abin da zai taimaka wa bangon ko da ace an yi gobara, ba za ta ci gidan ba.