Koma ka ga abin da ke ciki

Rumbun Hotunan Warwick na 3 (Janairu Zuwa Afrilu 2015)

Rumbun Hotunan Warwick na 3 (Janairu Zuwa Afrilu 2015)

A wannan rumbun hotunan, za ka ga ci gabar da aka samu daga Janairu zuwa Afrilu 2015, a aikin da ake yi a sabuwar hedkwatar Shaidun Jehobah.

Hoton da ke nuna yadda hedkwata ta Warwick za ta kasance idan aka kammala. Somawa daga hagu:

  1. Gidan Gareji

  2. Wajen Ajiye Mota don Baki

  3. Gidan Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

  4. Gidan Zama na B

  5. Gidan Zama na D

  6. Gidan Zama na C

  7. Gidan Zama na A

  8. Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

2 ga Janairu, 2015​—Gidan Gareji

Wani mataimakin Kwamitin Buga Littattafai na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah mai suna Harold Corkern ya ba da wani jawabi daga Littafi Mai Tsarki mai jigo “Cim ma Makasudinku.” (Living Up to Your Potential) Masu ba da jawabi suna ziyarar Warwick a kai a kai don su karfafa ma’aikatan.

14 ga Janairu, 2015​—Ofisoshi/Wuraren Hidimomi

Wannan farin tamfal yana kāre ma’aikatan kuma yana taimaka musu su cim ma aikinsu a lokacin da ake matsanancin dari. A wannan bangare na ginin ne za a saka gidan cin abinci da sashen kula da marasa lafiya da kicin da kuma sashen wanki.

16 ga Janairu, 2015​—Gidan Zama na D

Masu gyaran wuta suna shirin saka wayar lantarki. Tsawon wayar wuta da aka warware a cikin gidajen zama ya wuce kafa 40,000. Da zarar an sayi filin Warwick, sai aka soma aikin gyaran wuta kuma za a ci gaba da yin hakan har sai an kammala aikin gine-ginen.

16 ga Janairu, 2015​—Gidan Zama na A

Wani ma’aikaci yana rufe baranda da wani irin tef mai gam (duct tape) don hana ruwa shiga. A nan, ana rufe barandan da suke sama da wani kayan aiki mai nau’in ruwa don hana wurin jikewa. Ana kiran wannan kayan aikin polymethyl methacrylate.

23 ga Janairu, 2015​—Gidan Zama na A

Wani mahaifi da diyarsa, masu gyaran wuta suna saka wayoyin da za su kai wutar lantarki zuwa gidajen zama.

6 ga Fabrairu, 2015​—Gidan Gareji

Ma’aikata suna cin abincin rana a gidan cin abinci da aka gina na dan lokaci. A kowace rana, ana ba da abincin rana fiye da kwanuka 2,000.

12 ga Fabrairu, 2015​—Gidan Gyare-Gyare da Kuma Wajen Ajiye Mota don Mazauna

Masu aikin ayon benda suna saka karafuna a harsasin gini, inda za a gina shaguna don yin gyare-gyare.

12 ga Fabrairu, 2015​—Gidan Zama na C

Wasiku da yara suka rubuta don nuna godiyarsu ga ma’aikatan. Masu taimakawa da yawa suna zuwa su yi aiki a Warwick na dan lokaci. Ana samun sababbin ma’aikata kimanin 500 kowane mako. A watan Fabrairu, wajen mutane 2,500 ne suka yi aiki a Warwick kowace rana.

24 ga Fabrairu, 2015​—Yadda Aiki Yake Ci-gaba a Warwick

An gama wajen kashi 60 na aikin gine-ginen yanzu. Daga Janairu zuwa Afrilu 2015, an gama tsara yadda gidajen zama za su kasance. Kari ga haka, an kammala aikin ayon benda a ginin da ke dauke da Ofisoshi da Wuraren Hidimomi. Har ila, a wannan lokacin ne ma’aikata suka soma kafa bangwayen kankare a Gidan Gyare-Gyare, sun gina hanyoyin tafiya tsakanin gidajen zama kuma sun gyara wani dam a tafkin da ake kira Sterling Forest Lake ko kuma Blue Lake.

25 ga Fabrairu, 2015​—Ofisoshi da Wuraren Hidimomi

Yadda dakin da za a saka matakala a ciki yake daga kasa. ’Yan kwagila sun gina irin wadannan dakuna don saka matakala. Kowane dakin matakala yana da tsawon bene mai hawa biyar. Shaidun Jehobah ne suka taimaka wajen zuba kankaren.

26 ga Fabrairu, 2015​—Gidan Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

Wata rana da aka yi sanyi sosai, masu aikin ayon benda suna saka karafuna a hawa na fari. Dusar kankara da aka yi a Warwick daga Janairu zuwa Maris ya kusan inci 50. Mutane masu share dusar kankara sun yi ta tsabtace wuraren aikin kuma an saka wani na’ura mai tanadar da iska mai zafi don ma’aikatan su ji dumi.

12 ga Maris, 2015​—Wajen Ajiye Mota don Baki

An kera da karafuna kuma aka rufe da kwanon karfe. A karshen Afrilu, an gama yawancin rufin na gidajen zama kuma an kafa su. A watan Yuni ne aka kafa rufin na Gidan Zama na B. Wannan shi ne rufin na karshe da aka saka.

18 ga Maris, 2015​—Gidan Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

Yadda wurin yake daga cikin injin mai daga kaya wato, tower crane da ke fuskantar Gidan Zama na B.

18 ga Maris, 2015​—Gidan Gyare-Gyare da Wajen Ajiye Mota don Mazauna

Masu aikin famfo suna duba zane a Wajen Ajiye Mota don Mazauna. Zane-zanen da ake bukata don kammala aikin gaba daya sun wuce 3,400.

23 ga Maris, 2015​—Ofisoshi/Wuraren Hidimomi

Ma’aikata a cikin inji mai daga mutum sama (boom lift) suna saka tamfal don su kāre ginin. An gudanar da azuzuwa dabam-dabam don horar da ma’aikata su san yadda ake amfani da injuna da kuma na’urorin da kyau. Azuzuwan kiyaye hadari da aka gudanar sun kunshi na yadda za yi amfani da inji mai daga mutane sama, da na kiyaye mutum daga faduwa, da na yadda ake yin amfani da kayan numfashi, da kafa injunan masu dauka kaya da dai sauransu.

30 ga Maris, 2015​—Yadda Aiki Yake Ci-gaba a Warwick

Wannan hoton yana fuskantar yamma inda gidajen zama suke. A karshen watan Afrilu, an soma aikin wuta da kuma fanfo a gidajen zama na A da B da kuma D kamar yadda aka nuna a hoton nan. A gidan zama na C (hoton ba ya nan), an soma toshe ramukan da ke jikin bango da saka tayil da kuma fenti.

15 ga Afrilu, 2015​—Gidan Zama na B

Wasu ma’aikata biyu a kan inji mai daga mutane sama (boom lift), suna shafa fenti mai hana danshi a jikin bangon waje. Shafa wannan fenti mai hana danshi a kowane gidan zama yana daukan wajen wata biyu.

27 ga Afrilu, 2015​—Ofisoshi/Wuraren Hidimomi

Magina suna gina bango da bulo na dutse. A wannan sashe na ginin ne za a gina wurin gudanar da wasu hidimomin taimako da kuma wurin karban kayayyakin da ake kawowa.

30 ga Afrilu, 2015​—Yadda Aiki Yake Ci-gaba a Warwick

Wani mai shigar ruwa da aka yi hayarsa yana saka sabuwar na’urar bude inda ruwa yake bi bayan ya cire tsohuwar. Yanzu, ta wajen amfani da na’ura, za a iya rage yawan ruwan da ke tafkin (Blue Lake) don a hana ambaliyar ruwa awkuwa sa’ad da aka yi guguwar ruwa da iska.