Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Wakokin JW

Zan Sake Tashi

Zan Sake Tashi
DUBA
Kalma
Hoto

Ka saukar:

 1. 1. Bakin cikin da nake yi na ci min rai.

  Jehobah, na san na yi kuskure.

  Ina son karfi don in rika bauta maka.

  Ina so in dawo kungiyarka.

  (AMSHI)

  Duk dokokinka Jehobah​—ban manta su ba​—

  Gaskiyar da ke cikin Kalmarka.

  Ta ce ko na bijire, na yi tuntube,

  Zan sake tashi.

 2. 2. Na san da masu kaunata,

  Da sun damu da ni,

  Mutanen da ke son Jehobah.

  Kalmarka haske ce, za ta sa in dawo hanya.

  Hanyar rai na har abada ke nan.

  (AMSHI)

  Duk inda na je, abin da na ji, na tuna min cewa:

  Karshe yana kusa.

  (AMSHI)

  Ya Jehobah, Ubana, ka ji rokona

  Ina matukar son taimakonka.

  Ko da na yi tuntube sau da yawa,

  Zan iya tashi.

  (AMSHI)

  Allah Jehobah ya san ni; ina son taimakonsa fa.

  Ya san da kasawata kuma ya san ni sosai.

  Yana ganin amincina.

  (AMSHI)

  Zan je taro yau da yamma don in ga ’yan’uwana,

  Wurin da ya dace da ni.

  Kuma ko na bijire, na yi tuntube, zan sake tashi.

  Zan sake tashi.