DUBA

Ka saukar:

 1. 1. Jehobah, mahaliccin sama,

  Sama ya yi maka kaɗan.

  Balle ma a ce duniyar nan,

  Amma ruhunka yana nan.

  Mutanen da ke bin haskenka

  Suna daraja wurin nan.

  Muna murna don haɗin kanmu;

  Kana jin daɗin bautarmu.

  (AMSHI)

  Dukan arzikinmu

  Kai ka tanadar mana.

  Wannan gudummawarmu

  Asali naka ne.

  (AMSHI)

  Muna godiya don aikinka;

  Yanzu muna rera waƙa.

  Domin ka sa mun iya gina

  Wurin da zai ɗaukaka ka.

 2. 2. Jehobah, ka san bukatarmu

  Muna bukatar gu mai kyau

  Inda za mu riƙa bauta ma

  Don mu sa wasu su san ka.

  Bari a yi nufinka a nan.

  Akwai ayyuka da yawa,

  Da Ɗanka ya ba mu domin mu

  Yi tafiya tare da kai.

  (AMSHI)

  Da dukan zuciya

  Muna maka hidima.

  Kai kaɗai ka cancanta—

  Kai ne mai alheri.

  (AMSHI)

  Muna godiya don aikinka;

  Yanzu muna rera waƙa.

  Domin ka sa mun iya gina

  Wurin da zai ɗaukaka ka.