DUBA

Ka saukar:

 1. 1. Mene ne zan yi? Waye ne zan bi?

  Kila zuwa wurin ba wani laifi ba.

  Zan iya mutunta su, idan na bi su.

  Wai, wane zabi ne zan yi? Waye ne zan bi?

  Mene zan yi? Shawarar wa zan bi?

  Watakila su wuce gona da iri​—

  Za su iya yin abubuwa marar kyau.

  Wai, wane zabi ne zan yi? Jehobah, ka ji rokona.

  (AMSHI)

  Ina son dokarka, ina bin ta sosai.

  Zan daraja ta a kowane lokaci.

  Ka taimaka mini in bi duk dokokin da ke Kalmarka.

 2. 2. Na san ka’idarka. Zan bincika sosai.

  Ba na so in sa su yi bakin ciki fa,

  Amma kila su karya dokokin Allah.

  Na san abin da ke da kyau​—⁠da Jehobah ke so.

  (AMSHI)

  Ina son dokarka, ina bin ta sosai.

  Tana taimaka mini yin abu mai kyau.

  Ka taimaka mini in bi duk dokokin da ke Kalmarka.

  (AMSHI)

  Ina son dokarka, ina bin ta sosai.

  Tana taimaka mini yin abu mai kyau.

  Karanta ta na haskaka rayuwata.

  Na san kana tare da ni a koyaushe.

  Ka taimaka mini in bi duk dokokin da ke Kalmarka.