Ka saukar:

 1. 1. A kowace rana fa, muna zabi

  Domin mu kasance masu ibada.

  Akwai lokuta na, yin farin ciki

  Amma ba shi ne ya fi muhimmanci ba.

  (AMSHI)

  Sai mu nemi lokaci a kowace rana

  Don Addu’a, koyo da bauta.

  Yin nufin Allah, shi ya fi muhimmanci.

  Kada mu yi sanyin gwiwa.

  Mu tuna aljanna don ta yi kusa.

  Kar wani abu ya dauke hankalinmu.

 2. 2. Akwai matsaloli a rayuwa.

  Za su iya sa mu, rashin bangaskiya.

  Iyalinmu na bukatarmu.

  Idan muna son mu taimaka ma yaranmu

  (AMSHI)

  Sai mu nemi lokaci a kowace rana

  Don Addu’a, koyo da bauta.

  Yin nufin Allah, shi ya fi muhimmanci.

  Kada mu yi sanyin gwiwa.

  Mu tuna aljanna don ta yi kusa.

  Kar wani abu ya dauke hankalinmu.

  (AMSHI)

  Sai mu nemi lokaci a kowace rana

  Don Addu’a, koyo da bauta.

  Yin nufin Allah, shi ya fi muhimmanci.

  Kada mu yi sanyin gwiwa.

  Mu tuna aljanna don ta yi kusa.

  Kar wani abu ya dauke hankalinmu.