DUBA
Kalma

(Zabura 25:4)

 1. 1. Mun taru a nan ya Jehobah Allah,

  Domin kai ne ka gayyato mu.

  Kalmarka tana nuna mana hanya,

  Tana sa mu san dokokinka.

  (AMSHI)

  Ka koya min, domin in fahimta;

  Ka sa na riƙa bin umurninka.

  Ka taimaka min in yi nagarta,

  Kuma in so dokokinka sosai.

 2. 2. Hikimarka babu iyaka, Allah;

  Hukuncinka babu kuskure.

  Duk umurninka na da ban mamaki;

  Kalmarka tana ƙarfafa mu.

  (AMSHI)

  Ka koya min, domin in fahimta;

  Ka sa na riƙa bin umurninka.

  Ka taimaka min in yi nagarta,

  Kuma in so dokokinka sosai.

(Ka kuma duba Fit. 33:13; Zab. 1:2; 119:27, 35, 73, 105.)