Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

'Ku Rera Waka da Murna' ga Jehobah—Kalmomi Kadai

 WAƘA TA 79

Ku Koya Musu Su Kasance da Aminci

Ka Zabi Sauti
Ku Koya Musu Su Kasance da Aminci
DUBA
Kalma

(Matta 28:19, 20)

 1. 1. Tumakin Jehobah Allahnmu

  Sun girma, muna murna.

  Allah ya kula da su sosai

  Don suna bauta masa.

  (AMSHI)

  Jehobah, ka ji roƙonmu

  Ka kuma kāre su sosai.

  Mun roƙa ta sunan Yesu: Don su tsira;

  Su kuma riƙe aminci.

 2. 2. Muna yin addu’a domin su,

  Kar su yi sanyin gwiwa.

  A kullum muna koyar da su;

  Hakan na ƙarfafa su.

  (AMSHI)

  Jehobah, ka ji roƙonmu

  Ka kuma kāre su sosai.

  Mun roƙa ta sunan Yesu: Don su tsira;

  Su kuma riƙe aminci.

 3. 3. Ka sa duk su dogara da kai,

  Da kuma Ɗanka Kristi.

  Su jimre su fa yi biyayya,

  Don su tsira da ransu.

  (AMSHI)

  Jehobah, ka ji roƙonmu

  Ka kuma kāre su sosai.

  Mun roƙa ta sunan Yesu: Don su tsira;

  Su kuma riƙe aminci.

(Ka kuma duba Luk. 6:48; A. M. 5:42; Filib. 4:1.)