DUBA

(Zabura 19)

 1. 1. Sammai suna ɗaukaka ikon Allah.

  Ayyukan hannunsa,

  mun ga a sarari.

  Suna sa mu yabe shi a kullum.

  Taurari da suke sama,

  sun nuna ƙaunarsa.

 2. 2. Kalmar Allah za ta sa mu sami rai,

  Umurnansa suna

  sa mu yi hikima.

  Shi Sarki ne da ke yin adalci.

  Kalmominsa da dokarsa,

  suna da daɗin bi.

 3. 3. Har abada za mu bauta wa Allah.

  Dokokinsa kuma

  sun fi zinariya.

  Kiyaye su zai sa mu sami rai.

  Ƙaunarsa da ɗaukakarsa,

  za mu yi shelar su.

(Ka kuma duba Zab. 111:9; 145:5; R. Yoh. 4:11.)