Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

'Ku Rera Waka da Murna' ga Jehobah—Kalmomi Kadai

 WAƘA TA 58

Muna Neman Mutane Masu Saukin Kai

Ka Zabi Sauti
Muna Neman Mutane Masu Saukin Kai
DUBA
Kalma

(Luka 10:6)

 1. 1. Yesu ya ce mu riƙa wa’azi.

  Ko da rana, ko da iska, ya yi wa kowa wa’azi.

  Ya yi hakan don yana ƙaunar su.

  Ya yi shela daga safe har zuwa yamma.

  Muna zuwa gida-gida,

  Domin mu gaya wa kowa

  Allah ya kusan cire wahaloli.

  (AMSHI)

  Muna zuwa

  Yaɗa bisharar Mulkin Allah,

  Muna neman

  Waɗanda ke son samun ceto,

  Ba ma so mu

  Ƙyale kowa.

 2.  2. Muna bisharar Mulkin da ƙwazo.

  Maƙwabtanmu, da danginmu, muna so su san gaskiya.

  Ƙauna ce ta sa muke yin hakan.

  Mu riƙa taimakon su su bauta wa Allah.

  Muna shela a ko’ina,

  Kuma muna farin ciki,

  Idan wasu suna son wa’azinmu.

  (AMSHI)

  Muna zuwa

  Yaɗa bisharar Mulkin Allah,

  Muna neman

  Waɗanda ke son samun ceto,

  Ba ma so mu

  Ƙyale kowa.

(Ka kuma duba Isha. 52:7; Mat. 28:19, 20; Luk. 8:1; Rom. 10:10.)