DUBA
Kalma

(1 Timotawus 2:4)

 1. 1. Muna so mu yi koyi da Allah,

  Shi ba ya nuna wa kowa son kai.

  Yana son kowa ya sami ceto;

  Yana son kowa ya bauta masa.

  (AMSHI)

  Mutum ne ba yare ba;

  Zuci ne ba fuskar ba.

  Za mu yaɗa bishara ga kowa.

  Don muna son su sosai,

  Muna zuwa ko’ina:

  ‘Don mutane su bauta wa Allah.’

 2. 2. Za mu yi wa’azi a ko’ina

  Mu yi ko yaya kamarsu take.

  Halinsu ne ke da muhimmanci—

  Zuciya ce Allah yake gani.

  (AMSHI)

  Mutum ne ba yare ba;

  Zuci ne ba fuskar ba.

  Za mu yaɗa bishara ga kowa.

  Don muna son su sosai,

  Muna zuwa ko’ina:

  ‘Don mutane su bauta wa Allah.’

 3. 3. Allah na son masu bauta masa,

  Da suka ƙi halin duniyar nan.

  Don haka ne, muke yin wa’azi,

  Ga dukan mutanen da za su ji.

  (AMSHI)

  Mutum ne ba yare ba;

  Zuci ne ba fuskar ba.

  Za mu yaɗa bishara ga kowa.

  Don muna son su sosai,

  Muna zuwa ko’ina:

  ‘Don mutane su bauta wa Allah.’

(Ka kuma duba Yoh. 12:32; A. M. 10:34; 1 Tim. 4:10; Tit. 2:11.)