Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

'Ku Rera Waka da Murna' ga Jehobah—Kalmomi Kadai

 WAƘA TA 56

Ka Rike Gaskiya

Ka Zabi Sauti
Ka Rike Gaskiya
DUBA
Kalma

(Misalai 3:1, 2)

 1. 1. Bauta wa Allah shi ne abu mafi kyau,

  Amma kai ne za ka yi zaɓin.

  Don haka ka bi dukan umurnin Allah;

  Ka amince da Kalmarsa.

  (AMSHI)

  Ka bauta masa.

  Ka yi da duk zuciya.

  Jehobah zai yi

  Maka albarka

  In ka riƙe gaskiya.

 2. 2. Duk ƙoƙarinka da ayyukan da ka yi

  A bautar Allah da Mulkinsa

  Za su sa Allah ya yi maka albarka,

  Ka sami rai har abada.

  (AMSHI)

  Ka bauta masa.

  Ka yi da duk zuciya.

  Jehobah zai yi

  Maka albarka

  In ka riƙe gaskiya.

 3. 3. Dukanmu kamar yara ne wurin Allah

  Dole mu bi ja-gorancinsa.

  Ka yi tafiya da Ubanmu na sama;

  Don ka sami albarkarsa.

  (AMSHI)

  Ka bauta masa.

  Ka yi da duk zuciya.

  Jehobah zai yi

  Maka albarka

  In ka riƙe gaskiya.

(Ka kuma duba Zab. 26:3; Mis. 8:35; 15:31; Yoh. 8:31, 32.)