Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

'Ku Rera Waka da Murna' ga Jehobah—Kalmomi Kadai

 WAƘA TA 55

Kada Ku Ji Tsoron Su!

Ka Zabi Sauti
Kada Ku Ji Tsoron Su!
DUBA
Kalma

(Matta 10:28)

 1. 1. Ku ci gaba, Ya bayina,

  Ku yi wa’azin Mulkin.

  Kada ku ji tsoron su.

  Ku gaya wa mutane

  Cewa Ɗana, Yesu Kristi,

  Ya yi yaƙi da Shaiɗan,

  Kuma za ya halaka shi,

  Dukanmu za mu huta.

  (AMSHI)

  Kar ku ji tsoro bayina,

  Ko sun yi barazana.

  Zan riƙa kāre bayina

  Kamar ƙwayar idona.

 2. 2. Ko da suna nan da yawa,

  Suna hamayya da ku,

  Ko da sun yi murmushi,

  Domin su yaudare ku.

  Kar ku ji tsoro bayina,

  Ko sun tsananta muku,

  Don zan kāre mai aminci

  A yaƙin Armageddon.

  (AMSHI)

  Kar ku ji tsoro bayina,

  Ko sun yi barazana.

  Zan riƙa kāre bayina

  Kamar ƙwayar idona.

 3.  3. Ni ba zan manta da ku ba;

  Ni ne madogaranku.

  Ko da kun rasa ranku,

  Zan iya tayar da ku.

  Kar ku ji tsoron ʼyan Adam

  Ba za su kashe ku ba.

  In kuka riƙe aminci;

  Zan yi muku albarka!

  (AMSHI)

  Kar ku ji tsoro bayina,

  Ko sun yi barazana.

  Zan riƙa kāre bayina

  Kamar ƙwayar idona.

(Ka kuma duba K. Sha. 32:10; Neh. 4:14; Zab. 59:1; 83:2, 3.)