DUBA
Kalma

(Ishaya 30:20, 21)

 1. 1. Akwai wata hanya,

  Hanyar salama ce.

  Hanyar tana cikin,

  Littafi Mai Tsarki,

  Kuma Yesu ya koyar

  Da wannan hanyar.

  Kuma muna cikin,

  Wannan hanyar a yau.

  (AMSHI)

  Ga hanyar rai a nan; Ga hanyar rai.

  Kar ka bar ta; komin jarrabawa!

  Allah na kira: ‘Ga hanyar rai;

  Kar ka bar ta, domin, hanyar rai ce.’

 2. 2. Akwai hanyar ƙauna,

  Wanda ba irin ta.

  Nufin Allah shi ne

  Mu bi wannan hanyar.

  Don shi mai ƙauna ne;

  Da kuma gaskiya.

  Hanyar ƙauna da rai;

  Da kuma salama.

  (AMSHI)

  Ga hanyar rai a nan; Ga hanyar rai.

  Kar ka bar ta; komin jarrabawa!

  Allah na kira: ‘Ga hanyar rai;

  Kar ka bar ta, domin, hanyar rai ce.’

 3.  3. Akwai wata hanya,

  Ta rai har abada.

  Kamar yadda Allah:

  Ya yi alkawari,

  Babu wata hanya,

  Kamar wannan hanyar.

  Ga hanyar rai a nan,

  Allah mun gode ma.

  (AMSHI)

  Ga hanyar rai a nan; Ga hanyar rai.

  Kar ka bar ta; komin jarrabawa!

  Allah na kira: ‘Ga hanyar rai;

  Kar ka bar ta, domin, hanyar rai ce.’

(Ka kuma duba Zab. 32:8; 139:24; Mis. 6:23.)