Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

'Ku Rera Waka da Murna' ga Jehobah—Kalmomi Kadai

 WAƘA TA 5

Ayyukan Allah Suna da Ban Al’ajabi

Ka Zabi Sauti
Ayyukan Allah Suna da Ban Al’ajabi
DUBA
Kalma

(Zabura 139)

 1. 1. Allah, kai ne ka san ni sosai, Ka san dukan abin da nake yi.

  Kana ganin kome a zuciyata, furucina, halayena,

  duk ka san su.

  Ka ga sa’ad da nake ciki, Kuma ka ga duk ƙasusuwana.

  Fasalina duk a rubuce suke. Ina yabo da kuma son

  ayyukanka.

  Hikimarka tana da ban mamaki; Ina farin cikin sanin hakan.

  Idan na ɓoye a wuri mai duhu,

  Duk da haka Jehobah zai gan ni.

  Jehobah a ina zan ɓoye, da ba za ka iya gani na ba?

  Ko na shiga Kabari ko a sama, ko cikin duhu ko teku;

  za ka gan ni.

(Ka kuma duba Zab. 66:3; 94:19; Irm. 17:10.)