DUBA
Kalma

(Zabura 4:1)

 1. 1. Ya Jehobah ina roƙo ka ji: “Addu’ata.”

  Damuwata sun yi yawa; za su fi ƙarfina.

  Matsalolin rayuwa suna sa baƙin ciki.

  Ya Allah ka taimake ni; don in yi nasara.

  (AMSHI)

  Taimake ni; don in jimre.

  In na gaji, taimake ni.

  Ina roƙo, don ƙuncina.

  Ya Allahna, ji roƙona.

 2. 2. Ina karanta Kalmarka lokacin damuwa

  Domin tana kwantar mini da hankali sosai.

  Bari ta sa na gaskata da alkawuranka.

  Domin in riƙa ƙaunar ka cikin rayuwata.

  (AMSHI)

  Taimake ni; don in jimre.

  In na gaji, taimake ni.

  Ina roƙo, don ƙuncina.

  Ya Allahna, ji roƙona.

(Ka kuma duba Zab. 42:6; 119:28; Rom. 8:26; 2 Kor. 4:16; 1 Yoh. 3:20.)