DUBA
Kalma

(Mai Wa’azi 7:1)

 1. 1. Duk rayuwarmu, a kullum muna so

  Mu riƙa yi wa Jehobah biyayya.

  In muna yin abin da Allah yake so,

  Za mu faranta wa Allah rai.

 2. 2. Shaiɗan ya fi so mu nemi ɗaukaka,

  Har da arziki, a wannan duniyar.

  Amma duk wofi ne, in mun so duniya,

  Ba za mu sami albarkar ba.

 3. 3. Muna so Allah ya amince da mu

  Domin mu sami rai na har abada.

  Mu dogara da shi, mu kāre sunansa

  Kuma mu riƙe amincinmu.

(Ka kuma duba Far. 11:4; Mis. 22:1; Mal. 3:16; R. Yoh. 20:15.)