DUBA

(Zabura 55)

 1. 1. Ina so in kusace ka,

  Ya Jehobah Allahna.

  Allah ka taimaka mini

  Don in daina jin tsoro.

  (AMSHI)

  Ka dogara ga Jehobah,

  Zai kula da kuma cece ka.

  Allah zai kāre ka kullum

  Don shi mai aminci ne.

 2. 2. Da ina da fukafukai,

  Zan guje wa masifa.

  Zan gudu daga mugaye

  Don kada su kama ni.

  (AMSHI)

  Ka dogara ga Jehobah,

  Zai kula da kuma cece ka.

  Allah zai kāre ka kullum

  Don shi mai aminci ne.

 3. 3. Ƙarfafa daga Jehobah

  Na kwantar mana da rai.

  Zai taimake mu mu jimre.

  Shi Allah ne mai ƙauna.

  (AMSHI)

  Ka dogara ga Jehobah,

  Zai kula da kuma cece ka.

  Allah zai kāre ka kullum

  Don shi mai aminci ne.

(Ka kuma duba Zab. 22:5; 31:1-24.)