DUBA

(Fitowa 32:26)

 1. 1. Dā can muna yawo cikin duhu,

  Mun bi koyarwar addinan ƙarya.

  Amma yanzu mun koyi gaskiya,

  Gaskiyar Mulkin Allah.

  (AMSHI)

  Mu bauta wa Allah, Allah Jehobah.

  Ba zai ƙyale mu ba; mu bi haskensa.

  Mu yaɗa wa kowa bisharar ’yanci.

  Mulkin Yesu Kristi, za ya dawwama.

 2. 2. Muna goyon bayan Mulkin Allah.

  Muna wa’azi a duk duniya.

  Yanzu ne lokaci na yin zaɓi,

  Zaɓin bauta wa Allah.

  (AMSHI)

  Mu bauta wa Allah, Allah Jehobah.

  Ba zai ƙyale mu ba; mu bi haskensa.

  Mu yaɗa wa kowa bisharar ’yanci.

  Mulkin Yesu Kristi, za ya dawwama.

 3. 3. Ba mu jin tsoron dabarun Shaiɗan,

  Domin Jehobah za ya kāre mu.

  Ko da maƙiya sun fi mu yawa,

  Mun dogara ga Allah.

  (AMSHI)

  Mu bauta wa Allah, Allah Jehobah.

  Ba zai ƙyale mu ba; mu bi haskensa.

  Mu yaɗa wa kowa bisharar ’yanci.

  Mulkin Yesu Kristi, za ya dawwama.

(Ka kuma duba Zab. 94:14; Mis. 3:5, 6; Ibran. 13:5.)