DUBA

(Zabura 15)

 1. 1. Jehobah Allahnmu,

  Waye abokinka?

  Waye amini mai aminci?

  Da ya san ka sosai?

  Duk mai bin Kalmarka,

  Duk mai bangaskiya,

  Duk mai aminci, mai adalci,

  Mai faɗin gaskiya.

 2. 2. Jehobah Allahnmu,

  Wa zai kusace ka?

  Waye ke faranta maka rai?

  Da ka san sunansa?

  Duk mai daraja ka,

  Da ke bin Dokarka,

  Duk mai aminci, mai adalci,

  Mai faɗin gaskiya.

 3. 3. Jehobah Allahnmu,

  Ka ji duk roƙonmu.

  Ka sa mu kusace ka sosai,

  Mu shaida ƙaunarka,

  Mu abokanka ne.

  Don muna ƙaunar ka.

  Babu abokin da zai fi ka,

  Kai ne abokinmu.

(Ka kuma duba Zab. 139:1; 1 Bit. 5:6, 7.)