Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

'Ku Rera Waka da Murna' ga Jehobah—Kalmomi Kadai

 WAƘA TA 18

Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

Ka Zabi Sauti
Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu
DUBA
Kalma
Hoto

(Luka 22:20)

 1. 1. Allah Jehobah yau,

  muna a gabanka,

  Don ka nuna mana ƙaunar

  da ba kamarta.

  Ka aiko da Ɗanka Yesu,

  don mu rayu.

  Babu wata sadaukarwa

  da ta kai wannan.

  (AMSHI)

  Ya ba da ransa dominmu.

  Ya yi hakan da jininsa.

  Har abada,

  za mu riƙa yi maka godiya.

 2. 2. Yesu ya yi sadaukarwar

  da son ransa.

  Ya ba da ransa domin

  yana ƙauna sosai.

  Yanzu muna da bege don

  ya cece mu.

  Muna da begen yin rayuwa,

  har abada.

  (AMSHI)

  Ya ba da ransa dominmu.

  Ya yi hakan da jininsa.

  Har abada,

  za mu riƙa yi maka godiya.

(Ka kuma duba Ibran. 9:13, 14; 1 Bit. 1:18, 19.)