DUBA

(Luka 5:13)

 1. 1. Da Kristi ya zo duniya,

  Ya nuna haƙuri sosai.

  Ya biya mana Dukan bukatunmu;

  Ya nuna mana ƙaunarsa.

  Ya warkar da naƙasassu,

  Guragu har da makafi.

  Kamar yadda zai yi a Mulkinsa

  Da ƙauna ya ce: “Na yarda.”

 2. 2. Muna yin koyi da Kristi

  A rayuwarmu koyaushe.

  Muna nuna ƙauna ga Duk mutane;

  Mun koya musu gaskiya.

  Muna taimakon waɗanda

  Suke cikin matsaloli.

  Idan marayu suka roƙe ka,

  Sai ka ce musu: “Na yarda.”

(Ka kuma duba Yoh. 18:37; Afis. 3:19; Filib. 2:7.)