DUBA

(Ibraniyawa 6:18, 19)

  1. 1. ’Yan Adam sun daɗe suna shan wahala,

    Ba za su iya taimakon kansu ba.

    Muna ganin hakan ta ayyukansu

    Domin dukansu ajizai ne.

    (AMSHI)

    Mu yi murna Mulkin Allah ya zo!

    Yesu Kristi zai ’yantar da dukanmu.

    Zai cire duk masu yin mugunta,

    Mu riƙe begen nan da ƙarfi sosai.

  2. 2. Mu sanar cewa ranar Allah na zuwa.

    Ba wanda zai ce wa Allah: “Har yaushe?”

    Domin zai ceci dukan halittunsa.

    Mu yabi Allah da waƙarmu.

    (AMSHI)

    Mu yi murna Mulkin Allah ya zo!

    Yesu Kristi zai ’yantar da dukanmu.

    Zai cire duk masu yin mugunta,

    Mu riƙe begen nan da ƙarfi sosai.

(Ka kuma duba Zab. 27:14; M. Wa. 1:14; Joel 2:1; Hab. 1:2, 3; Rom. 8:22.)