Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

'Ku Rera Waka da Murna' ga Jehobah—Kalmomi Kadai

 WAƘA TA 141

Rai, Kyauta Ce Daga Allah

Ka Zabi Sauti
Rai, Kyauta Ce Daga Allah
DUBA
Kalma

(Zabura 36:9)

 1. 1. Rai na ’yan Adam, da ruwan sama,

  Da kuma zafin rana, da abinci—

  Duka kyauta ce; Daga Allahnmu.

  Su ne suke sa mu ji daɗin rayuwa.

  (AMSHI)

  Amma, me za mu yi da rayuwarmu

  Mu riƙa so da kuma bauta wa Jehobah.

  Ba cancanta ba ce za ta ba mu rai ba.

  Domin rai kyauta ce—Kyauta daga Allah.

 2. 2. Wasu na kamar, matar Ayuba,

  Suna yin sanyin gwiwa don ƙuncinsu.

  Mu ba ma hakan; Za mu yabe shi,

  Mu kuma gode masa don rayuwarmu.

  (AMSHI)

  Amma, me za mu yi da rayuwarmu

  Mu riƙa so da kuma bauta wa Jehobah.

  Ba cancanta ba ce za ta ba mu rai ba.

  Domin rai kyauta ce—Kyauta daga Allah.

(Ka kuma duba Ayu. 2:9; Zab. 34:12; M. Wa. 8:15; Mat. 22:37-40; Rom. 6:23.)