Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

'Ku Rera Waka da Murna' ga Jehobah—Kalmomi Kadai

 WAƘA TA 14

Mu Yabi Sabon Sarkinmu

Ka Zabi Sauti
Mu Yabi Sabon Sarkinmu
DUBA
Kalma

(Zabura 2:12)

 1. 1. Ga mutane suna zuwa

  daga dukan al’ummai,

  Yesu ne ke tattara su

  cikin ikilisiya.

  Allah ya kafa Mulkinsa;

  Mulkin zai kawo albarka.

  Wannan bege ne mai tamani,

  Yana sa mu farin ciki.

  (AMSHI)

  Mu yabi Jehobah; Har da Ɗansa Kristi​—

  Don shi ne Sarkin Sarakuna.

  Mun zama talakawan Mulkinsa

  Mu ɗaukaka sunansa.

 2. 2. Mu yabi Kristi Sarkinmu,

  da waƙoƙin bakinmu.

  Shi zai yi sarauta kuma

  zai sa mu sami ceto.

  Yesu zai kawo albarka:

  Zai kuma cire mugunta;

  Kristi zai tayar da matattu.

  Lokacin za mu yi murna!

  (AMSHI)

  Mu yabi Jehobah; Har da Ɗansa Kristi​—

  Don shi ne Sarkin Sarakuna.

  Mun zama talakawan Mulkinsa

  Mu ɗaukaka sunansa.

(Ka kuma duba Zab. 2:6; 45:1; Isha. 9:6; Yoh. 6:40.)