DUBA

(Ru’ya ta Yohanna 21:1-5)

 1. 1. Ka ga kanka, ka gan ni ma;

  Ka gan mu duk a cikin aljanna.

  Yin rayuwa, a aljanna,

  Zai yi daɗi, kome zai yi kyau.

  Za a cire duk mugaye;

  Mulkin Jehobah zai dawwama.

  A lokacin da muke a aljanna,

  Za mu rera waƙa mu yabi Jehobah:

  (AMSHI)

  “Mun gode, Allah, don ayyukanka.

  Ɗanka Yesu ya gyara duniya.

  Muna godiya sosai don albarkarka;

  Muna rera waƙar yabo ga sunanka.”

 2.  2. Ka ga kanka, ka gan ni ma;

  Ka yi begen sabuwar duniya.

  Babu kome a duniya

  Da zai sa mu riƙa jin tsoro.

  Kalmominsa, duk sun cika;

  Albarkarsa na tare da mu.

  Allah zai tayar da dukan matattu;

  Dukanmu za mu rera yabo ga Allah:

  (AMSHI)

  “Mun gode, Allah, don ayyukanka.

  Ɗanka Yesu ya gyara duniya.

  Muna godiya sosai don albarkarka;

  Muna rera waƙar yabo ga sunanka.”

(Ka kuma duba Zab. 37:10, 11; Isha. 65:17; Yoh. 5:28; 2 Bit. 3:13.)