Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

'Ku Rera Waka da Murna' ga Jehobah—Kalmomi Kadai

 WAƘA TA 138

Tsofaffi Masu Aminci Suna da Daraja

Ka Zabi Sauti
Tsofaffi Masu Aminci Suna da Daraja
DUBA
Kalma

(Misalai 16:31)

 1. 1. Tare da tsofaffi ne,

  Muke ibada.

  Sun fuskanci wahala;

  Amma sun jimre.

  Yanzu ba su da ƙarfi;

  Ko sun kaɗaita.

  Allah, ka ba su ladar

  Rai a aljanna.

  (AMSHI)

  Ya Uba, ka tuna

  Da amincinsu.

  Bari su san cewa;

  Kana ƙaunarsu

 2. 2. Tsofaffi amintattu

  Masu daraja.

  Jehobah na ƙaunarsu

  Don amincinsu.

  Mu riƙa tuna cewa

  Dā su yara ne.

  Kuma sun yi hidima

  Da ƙwazo sosai.

  (AMSHI)

  Ya Uba, ka tuna

  Da amincinsu.

  Bari su san cewa;

  Kana ƙaunarsu

(Ka kuma duba Zab. 71:9, 18; Mis. 20:29; Mat. 25:21, 23; Luk. 22:28; 1 Tim. 5:1.)