DUBA

(Romawa 16:2)

 1. 1. Saratu, Esther, Maryam, Ruth, da sauran—

  Dukansu mata ne masu aminci.

  Suna ƙaunar Jehobah Allah sosai.

  Sun riƙe aminci, mun san sunansu.

  Ba a ambata sunan wasu ba

  A Kalmar Jehobah, su amintattu ne.

 2. 2. Matan suna da ƙauna da alheri—

  Har da bangaskiya da gaba gaɗi.

  Sun yi hidima da dukan zuciya.

  Sun kafa mana misalai masu kyau.

  A yau muna da ’yan’uwa mata

  Da ke nuna irin waɗannan halayen.

 3. 3. Iyaye mata, yara da gwauraye,

  Duk kuna hidima da ƙwazo sosai.

  Kuna ladabi da kuma biyayya.

  Allah na ƙaunar ku, kar ku ji tsoro.

  ’Yan’uwa mata, bari Jehobah

  Ya albarkace ku da rai har abada.

(Ka kuma duba Filib. 4:3; 1 Tim. 2:9, 10; 1 Bit. 3:4, 5.)