DUBA

(Ruth 2:12)

 1. 1. Jehobah ya san da dukan bayinsa

  masu yi masa biyayya.

  Ya san da sadaukarwar da suka yi

  Don su iya bauta masa.

  In ka bar iyalinka ko abokai,

  Ka san cewa Yana gani.

  Zai ba ka ’yan’uwa fiye da hakan

  Da kuma rai har abada.

  (AMSHI)

  Bari Allah ya albarkace ka.

  Don abubuwan da ka yi masa.

  Ka dogara gare shi sosai.

  Jehobah Allahnmu; mai aminci ne.

 2. 2. A wasu lokuta mukan ji kamar

  Wahalarmu ta yi yawa.

  Kuma mu ga kamar ba za mu iya

  Jimrewa da wahalar ba.

  Allah ya san da dukan bukatunmu;

  Zai kuma ji addu’armu.

  Zai ƙarfafa mu ta wurin Kalmarsa

  Da kuma abokan kirki.

  (AMSHI)

  Bari Allah ya albarkace ka.

  Don abubuwan da ka yi masa.

  Ka dogara gare shi sosai.

  Jehobah Allahnmu; mai aminci ne.

(Ka kuma duba Alƙa. 11:38-40; Isha. 41:10.)