DUBA

(Mai-Wa’azi 12:1)

 1. 1. Allah yana ƙaunar mu matasa,

  Mu bauta masa da duk ƙarfinmu.

  Don haka, zai riƙa kula da mu,

  Zai albarkace mu har abada.

 2. 2. Mu riƙa daraja iyayenmu

  Domin suna kula da mu sosai.

  Allah da mutane za su so mu

  Kuma za mu kusaci Jehobah.

 3. 3. Mu riƙa tunawa da Jehobah,

  Mu ci gaba da son koyarwarsa.

  Mu riƙa yin iya ƙoƙarinmu don hakan

  Zai sa Jehobah murna.

(Ka kuma duba Zab. 71:17; Mak. 3:27; Afis. 6:1-3.)