DUBA

(Matta 19:5, 6)

 1. 1. Allah ya haɗa su,

  Suna murna sosai.

  Kuma a gaban Allah

  Suka ɗau wa’adi.

  (AMSHI 1)

  Ya ce a gaban Allah,

  Za ya ƙaunace ta.

  ‘Jehobah ne ya haɗa,

  Kada mu raba su.’

 2. 2. A Kalmar Allah ce

  Suka san nufinsa,

  Sun nemi taimakonsa,

  Su cika wa’adin.

  (AMSHI 2)

  Ta ce a gaban Allah

  Za ta ƙaunace shi.

  ‘Jehobah ne ya haɗa,

  Kada mu raba su.’

(Ka kuma duba Far. 2:24; M. Wa. 4:12; Afis. 5:22-33.)