DUBA

(1 Bitrus 2:21)

 1. 1. Jehobah mai ƙauna

  Ya albarkace mu,

  Ya aiko Yesu domin ya cece mu.

  Ɗansa Yesu Kristi

  Ya zo duniyar nan,

  Don ya ɗaukaka Jehobah Allah.

 2. 2. Kalmar Jehobah ce

  Ta taimaki Yesu

  Ya zama mai hikima da basira.

  Ɗan Allah ya nuna

  Shi bawan kirki ne,

  Yana jin daɗin yin nufin Allah.

 3. 3. Mu bi misalin da

  Ɗan Allah ya kafa

  Don ayyukanmu su yabi Jehobah.

  Mu riƙa bin gurbin da

  Yesu ya kafa

  Domin mu more rai har abada.

(Ka kuma duba Yoh. 8:29; Afis. 5:2; Filib. 2:5-7.)