DUBA
Kalma

(1 Korintiyawa 16:13)

 1. 1. Mu yi tsaro mu yi ƙarfi,

  Kar mu daina jimrewa.

  Mu zama da ƙarfin hali,

  Domin mu yi nasara.

  Umurnin Yesu ne muke bi;

  Za mu bi shi babu fasawa.

  (AMSHI)

  Yi tsaro, ƙarfi, da aminci!

  Kar mu daina jimrewa!

 2. 2. Mu yi tsaro, da hikima,

  Mu riƙa yin biyayya.

  Mu bi ja-gorancin Kristi,

  Da bawa mai aminci.

  Mu yi wa dattawa biyayya,

  Su ne ke kāre bayin Allah.

  (AMSHI)

  Yi tsaro, ƙarfi, da aminci!

  Kar mu daina jimrewa!

 3.  3. Mu yi tsaro da haɗin kai,

  Mu riƙa yin wa’azi.

  Ko da mutane sun ƙi ji,

  Za mu riƙa wa’azi.

  Mu kai bishara a ko’ina.

  Ranar Jehobah ta yi kusa!

  (AMSHI)

  Yi tsaro, ƙarfi, da aminci!

  Kar mu daina jimrewa!

(Ka kuma duba Mat. 24:13; Ibran. 13:7, 17; 1 Bit. 5:8.)