DUBA

(Luka 17:5)

 1. 1. Domin ajizancinmu, Ya Jehobah,

  Muna yawan karya dokokinka.

  Abin da ke yawan jawo zunubi

  Shi ne rashin nuna bangaskiya.

  (AMSHI)

  Ƙarfafa bangaskiyarmu, Ya Allah.

  Taimake mu muna bukatar ta.

  Ƙarfafa bangaskiyarmu Jehobah

  Don mu riƙa yin nufinka kullum.

 2. 2. Sai da bangaskiya za mu bauta ma.

  Mun san za ka yi mana albarka.

  Ya Allahnmu, muna son taimakonka

  Don mu riƙa jimrewa har ƙarshe.

  (AMSHI)

  Ƙarfafa bangaskiyarmu, Ya Allah.

  Taimake mu muna bukatar ta.

  Ƙarfafa bangaskiyarmu Jehobah

  Don mu riƙa yin nufinka kullum.

(Ka kuma duba Far. 8:21; Ibran. 11:6; 12:1.)