DUBA
Kalma

(2 Bitrus 3:15)

 1. 1. Allah, Jehobah, mai iko ne,

  Kana son adalci sosai.

  Mun san ba ka farin ciki,

  Don wahalar da muke sha.

  Ka kusan halaka mugaye;

  Kai Allah ne mai yin adalci.

  (AMSHI)

  Mun ƙosa ganin ranar nan,

  Mu riƙa yaba maka kullum.

 2. 2. Kwana dubu wurin ’yan Adam,

  Na kamar ɗaya wurin ka.

  Ranarka ta kusa sosai;

  Za ta zo ran da kake so.

  Mun san ba ka son mugunta,

  Kana son mugu ya yi tuba.

  (AMSHI)

  Mun ƙosa ganin ranar nan,

  Mu riƙa yaba maka kullum.

(Ka kuma duba Neh. 9:30; Luk. 15:7; 2 Bit. 3:8, 9.)