Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 WAƘA TA 111

Dalilan da Suke Sa Mu Murna

Ka Zabi Sauti
Dalilan da Suke Sa Mu Murna
DUBA
Kalma

(Matta 5:12)

 1. 1. Muna da dalilai na murna,

  Da yawa babu iyaka.

  Mutane daga duk duniya

  Suna bauta wa Jehobah.

  Gaskiyar dake Kalmar Allah,

  Tana sa mu farin ciki.

  Shi ya sa muke nazarin ta;

  Domin mu kusaci Allah.

  Muna da dalilan yin murna,

  Daga cikin zuciyarmu.

  Ko da muna cikin wahala,

  Jehobah zai taimake mu.

  (AMSHI)

  Jehobah Allah mun gode,

  Duk ayyukanka na da kyau.

  Da hikimarka da ayyukanka,

  Suna sa mu farin ciki!

 2.  2. In mun lura da ayyukanka,

  Duniya, sararin sama.

  Da kuma sauran halittunka,

  Muna daraja sunanka.

  Muna koyar da duk duniya,

  Game da Mulkin Jehobah.

  Albarku da Mulkin zai kawo,

  Muna koya wa mutane.

  Za mu yi murna har abada,

  Za mu ji daɗin rayuwa

  Rayuwa a cikin aljanna

  Zai kawo albarka sosai.

  (AMSHI)

  Jehobah Allah mun gode,

  Duk ayyukanka na da kyau.

  Da hikimarka da ayyukanka,

  Suna sa mu farin ciki!

(Ka kuma duba K. Sha. 16:15; Isha. 12:6; Yoh. 15:11.)