DUBA

(Afisawa 4:8)

 1. 1. Allah ya ba mu makiyaya

  Don su kula da mu.

  Suna kafa misali mai kyau

  Da za mu riƙa bi.

  (AMSHI)

  Allah ya yi mana tanadi,

  Tanadin amintattu.

  Suna ƙauna da kula da mu.

  Mu ƙaunace su sosai.

 2. 2. Makiyayan nan na da ƙauna

  Da kuma sauƙin kai.

  In mun fuskanci matsaloli,

  Suna kula da mu.

  (AMSHI)

  Allah ya yi mana tanadi,

  Tanadin amintattu.

  Suna ƙauna da kula da mu.

  Mu ƙaunace su sosai.

 3. 3. Suna yi mana ja-goranci

  Don kar mu bijire,

  Don mu ci gaba da bauta wa

  Allahnmu koyaushe.

  (AMSHI)

  Allah ya yi mana tanadi,

  Tanadin amintattu.

  Suna ƙauna da kula da mu.

  Mu ƙaunace su sosai.

(Ka kuma duba Isha. 32:1, 2; Irm. 3:15; Yoh. 21:15-17; A. M. 20:28.)