Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

'Ku Rera Waka da Murna' ga Jehobah—Kalmomi Kadai

 WAƘA TA 10

Ku Yabi Jehobah Allahnmu!

Ka Zabi Sauti
Ku Yabi Jehobah Allahnmu!
DUBA
Kalma

(Zabura 145:12)

 1. 1. Yabi Jah! Yabi Allahnmu!

  Shaida sunansa ko’ina!

  Gaya wa, Duka mutane,

  Cewa Mulkinsa ya yi kusa.

  Jehobah ya ce lokaci ya yi

  Da Ɗansa zai zama Sarki.

  Ku je ku gaya wa duk mutane,

  Albarkun Mulkin Allahnmu!

  (AMSHI)

  Yabi Jah! Yabi Allahnmu!

  Shaida ikonsa a ko’ina!

 2. 2. Yabi Jah! Da farin ciki!

  Yi yabo ga sunan Allah!

  Yi hakan da duk zuciya,

  Mu yi shelar girman sunansa.

  Jehobah shi ne mai iko duka,

  Amma shi mai alheri ne.

  Ubanmu ya san duk bukatunmu;

  Yana amsa duk roƙonmu.

  (AMSHI)

  Yabi Jah! Yabi Allahnmu!

  Shaida ikonsa a ko’ina!

(Ka kuma duba Zab. 89:27; 105:1; Irm. 33:11.)