Waɗanne ƙalubale ne Hirudus ya fuskanta sa’ad da yake sake gina haikalin Urushalima?

Sulemanu ya gina haikalin Urushalima a kan tudu kuma ya yi katanga a sashen hankalin da ya fuskanci gabas da kuma yamma don a sami wurin wucewa kewaye da ginin. Hirudus ya so haikalin ya fi na Sulemanu girma, saboda haka, sai ya soma yin gyare-gyare da kuma faɗaɗa hankalin.

Magina da Hirudus ya ba wa aikin sun faɗaɗa filin da ke arewacin haikalin don hanyar ta daɗa faɗi. An faɗaɗa filin da ya fuskanci kudancin haikalin ya kai kafa 105, wato mita 32. Don su cim ma hakan, sun gina ganuwa na duwatsu. Akwai wuraren da tsawon ganuwar ta kai kafa 165, wato mita 50.

Hirudus bai so ya sa Yahudawa fushi ba ko kuma ya dakatar da ayyuka da kuma hadayar da ake yi a haikalin. Wani masanin tarihin Yahudawa mai suna Josephus ya ce Hirudus ya ma sa a koya wa firistocin Yahudawa aikin gini da kuma kafinta don kada wani da ba a yarda ya shiga wuri mai tsarki ya yi hakan.

Hirudus ya mutu kafin a kammala wannan aikin a shekara ta 30 bayan haihuwar Yesu, kuma a lokacin, an riga an yi shekara 46 ana ginin. (Yohanna 2:20) Tattaɓa-kunnen Hirudus mai suna Agaribas na Biyu ne ya kammala aikin a tsakiyar ƙarni na farko a zamanin Yesu.

Me ya sa mutanen Malita suka ga kamar Bulus mai kisan-kai ne?

Allahiyar adalci (a hagu) tana dūkan allahiyar rashin adalci

Babu shakka, koyarwar addinin Helenawa ta mamaye zuciyar wasu mutanen Malita. Ka yi la’akari da abin da ya faru bayan jirgin ruwa ya kife da su Bulus a Malita kamar yadda littafin Ayyukan Manzanni ya nuna. Sa’ad da manzon ya ƙara itace a wuta don abokan tafiyarsa su ci gaba da shan ɗumi, sai wani maciji mai dafi ya naɗe a hannunsa. Mazaunan tsibirin suka ce: “Babu shakka wannan mutum mai-kisan kai ne, kuma ko da yake ya tsira daga teku, shari’a ba ta barinsa ya yi rai ba.”Ayyukan Manzanni 28:4.

A Helenanci, kalmar nan “di’ke” tana da ma’ana biyu, wato “Adalci” da kuma allahiyar adalci. Sun ce allahiyar tana kula da harkokin ’yan Adam, tana kuma kai ƙarar mutanen da suka yi laifi a ɓoye wurin wani allah mai suna Zafsa don ya hukunta su. Saboda haka, wani littafi ya ce wataƙila mutanen Malita sun yi tunanin cewa: “Ko da yake Bulus ya tsira daga hatsarin jirgin ruwa, allahiyar Dike . . . ta gano laifuffukansa, shi ya sa ta aiko maciji ya naɗe a hannunsa.” Mutanen sun gano cewa ra’ayinsu ba daidai ba ne sa’ad da suka ga cewa macijin bai tsare Bulus ba.