Kafin ka kama yin wani abu, za ka iya cewa, ‘Yaya wannan abin zai amfane ni?’ Yin irin wannan tambayar game da addu’a son kai ne? A’a. Mutane suna yawan so su san ko addu’o’in da suke yi za su amfane su. Har Ayuba wanda shi mutumi ne mai aminci ya taɓa yin wannan tambayar: “Idan na kira shi, zai amsa ni kuwa?”—Ayuba 9:16, New World Translation.

A talifin da ya gabata, mun tattauna cewa addu’a ba abu ba ce da addinai suke yi kaɗai ba ko kuma kamar shan magunguna ba. Babu shakka, Allah na gaskiya yana jin addu’a. Idan muka yi addu’a a hanyar da ta dace kuma roƙonmu ya jitu da nufinsa, zai amsa mana. Hakika, ya umurce mu mu kusace shi. (Yaƙub 4:8) Ta yaya za mu amfana idan yin addu’a ya zama mana jiki? Bari mu tattauna wasu amfani da za mu samu.

Kwanciyar hankali.

Sa’ad da kake fuskantar matsaloli da ƙalubale, kana ƙyale alhini ya dame ka kuwa? Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa yin “addu’a ba fasawa” a irin waɗannan lokuttan, kuma mu ‘bar roƙe roƙenmu su sanu ga Allah.’ (1 Tasalonikawa 5:17; Filibiyawa 4:6) Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa idan muka yi addu’a ga Allah, ‘salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanmu da tunaninmu.’ (Filibiyawa 4:7) Za mu iya samun kwanciyar hankali idan muka gaya wa Ubanmu na sama damuwarmu. Ya ƙarfafa mu mu yi hakan a Zabura 55:22 cewa: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ka.”

“Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ka.”—Zabura 55:22

Mutane masu ɗimbin yawa a faɗin duniya sun sami wannan kwanciyar hankalin. Wata mai suna Hee Ran daga ƙasar Koriya ta Kudu, ta ce: “Kome tsananin matsalata, da zarar na yi addu’a, ina ji kamar  an magance matsalar kuma ina samun ƙarfin jimrewa.” Wata kuma mai suna Cecilia daga ƙasar Filifin, ta ce: “Da yake ni mahaifiya ce, ina tunani sosai game da ’ya’yana mata da mahaifiyata wadda ciwo da kuma tsufa suka sa ba ta gane ni kuma. Amma addu’a ta taimaka mini in daina yin alhini sosai. Na san cewa Jehobah zai taimaka mini in kula da su.”

Ta’aziyya da ƙarfin hali sa’ad da muke fuskantar gwaji.

Shin kana fuskantar matsaloli masu tsanani sosai ko kuma wani mawuyacin yanayi? Yin addu’a ga “Allah na dukan ta’aziyya” zai sa ka sami sauƙi. Littafi Mai Tsarki ya ce zai “yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.” (2 Korintiyawa 1:3, 4) Alal misali, lokacin da Yesu ya damu sosai, “ya durƙusa, ya yi addu’a.” Wane sakamako ya samu? “Mala’ika daga sama ya bayyana gare shi, yana ƙarfafa shi.” (Luka 22:41, 43)  Wani bawan Allah kuma mai suna Nehemiya ya sha wuya a hannun mugayen mutane da suka so su hana shi yin hidimar Allah. Ya yi addu’a, ya ce: “Ya Allah, ka ƙarfafa hannuwana.” Abin da ya faru bayan hakan ya nuna yadda Allah ya taimaka masa ya daina jin tsoro kuma ya kammala aikinsa. (Nehemiya 6:9-16) Wani mai suna Reginald daga ƙasar Gana ya yi bayani a kan abin da ya shaida don yin addu’a: “Idan na yi addu’a, musamman a lokacin da nake fuskantar yanayi mai wuya, ina ji cewa na furta matsalolina ga wani da ke da ikon taimaka mini, sai ya ce kada in yi fargaba.” Babu shakka, Allah zai iya ƙarfafa mu idan mun yi addu’a.

Hikima daga Allah.

Wasu zaɓin da muka yi za su iya shafanmu da ’yan’uwanmu da kuma abokanmu. Me zai taimaka mana mu riƙa yin zaɓi masu kyau? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan kowane a cikinku ya rasa hikima [musamman a lokacin da yake fuskantar gwaji], bari ya yi roƙo ga Allah, wanda yake bayar ga kowa a yalwace, ba ya tsautawa kuma; za a kuwa ba shi.” (Yaƙub 1:5) Idan mun roƙi Allah ya taimaka mana mu kasance da hikima, zai iya yin amfani da ruhunsa mai tsarki wajen taimaka mana mu yi zaɓi mai kyau. Za mu iya roƙon Allah ya ba mu ruhunsa mai tsarki domin Yesu ya ce ‘Ubanmu na sama za ya ba da Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda suke roƙonsa.’—Luka 11:13.

“Ina yin addu’a ga Jehobah a kai a kai don ya taimaka mini in yanke shawarar da ta dace.”—Kwabena, ƙasar Gana

Sa’ad da Yesu yake so ya yanke shawarwari masu muhimmanci, ya fahimce cewa yana bukata ya nemi taimako daga wurin Ubansa. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa sa’ad da yake so ya zaɓi manzanninsa 12, ya yi “dukan dare . . . yana addu’a ga Allah.”—Luka 6:12.

Mutane da yawa a yau suna kamar Yesu domin suna samun ƙarfafa sa’ad da Allah ya taimaka musu su yanke shawarwari masu kyau. Wata mai suna Regina daga ƙasar Filifin ta faɗi irin matsalolin da ta fuskanta bayan rasuwar maigidanta. Waɗannan matsalolin sun haɗa da biyan bukatunta da na yaranta, rasa aikinta da kuma ɗawainiyar renon yara. Mene ne ya taimaka mata ta yanke shawarwari masu kyau? Ta ce, “Na dogara ga Jehobah ta wajen yin addu’a.” Wani mai suna Kwabena daga ƙasar Gana ya faɗi dalilin da ya sa ya nemi taimakon Allah, “An kore shi daga aikin gine-gine da yake yi da ake biyan shi albashi mai tsoka.” Sa’ad da yake tunani a kan abin da zai yi, ya ce: “Ina yin addu’a ga Jehobah a kai a kai don ya taimaka mini in yanke shawarar da ta dace.” Ya kuma ce, “Na yi farin ciki domin Jehobah ya taimake ni in zaɓi aikin da zai ba ni damar yin ibada da kuma biyan bukatuna na yau da kullum.” Allah zai ja-gorance ka idan ka yi addu’a don kada kome ya ɓata dangantakarka da shi.

Mun ambata wasu amfani da za mu iya samu don yin addu’a. (Don samun ƙarin bayani, ka duba akwatin nan “ Amfanin Yin Addu’a.”) Amma idan kana so ka sami wannan amfanin, dole ne ka fara sanin Allah da kuma nufinsa. Idan abin da kake so ke nan, muna ƙarfafa ka ka gaya wa Shaidun Jehobah su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kai. * Abu na farko ke nan da kake bukata don ka kusaci “Mai jin addu’a.”—Zabura 65:2.

^ sakin layi na 14 Don Allah ka tuntuɓi Shaidun Jehobah a yankinku ko kuma ka ziyarci dandalinmu na www.jw.org/ha.